Kasashen Sin da Masar sun jaddada niyyarsu ta inganta dangantakar dake tsakaninsu karkashin tsarin kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO).
An bayyana hakan ne yayin wani taron karawa juna sani da ofishin jakadancin Sin dake Masar, da majalisar kula da harkokin waje ta kasar Masar suka shirya ranar Lahadi a birnin Alkahira. Taron ya samu mahalarta daga kasashen biyu da suka hada da manyan jami’an diplomasiyya da masana harkokin waje da ‘yan jarida.
- Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
A jawabinsa, jakadan Sin dake Masar Liao Liqiang, ya ce Masar abokiyar tattaunawa ce ta SCO, yana mai maraba da shigarta cikin harkoki daban-daban na SCO.
Ya ce yana sa ran Sin da Masar za su kara hada hannu karkashin tsare tsaren SCO da inganta dangantakar dake tsakaninsu domin cimma gina al’ummar Sin da Masar mai makoma ta bai daya a sabon zamani da bayar da gudunmuwa ga zaman lafiya da ci gaban duniya.
Shi kuwa daraktan majalisar kula da harkokin wajen Masar Ezzat Saad wanda ya jagoranci taron, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, har kullum, Masar ta kasance mai karfafa hadin gwiwa da Sin a matakin dangantakar dake tsakaninsu da ma na kungiyar SCO.
Su kuwa mahalarta taron, sun yaba da kyautatuwar dangantakar kasashen biyu da rawar da SCO ke takawa. Sun kuma bayyana fatan Masar da Sin za su yi amfani da damarmakin ci gaba da SCO ta samar domin su hada hannu tare, su inganta tsarin jagorantar harkokin duniya da farfadowar kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp