Yayin ziyarar aiki da firaministan Sifaniya Pedro Sanchez Perez-Castejon ya gudanar a kasar Sin a jiya Juma’a, an sanya hannu kan takardun yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin hukumar lura da harkokin fina-finai ta kasar Sin da takwararta ta kasar Sifaniya. Yarjejeniyar fahimtar junan dai na da nufin zurfafa musaya, da hadin gwiwa a fannin shirya fina-finai.
Yanzu haka kasar Sin ce ta biyu a girman kasuwar fina-finai ta duniya, kuma masu zuba jari da mashirya fina-finai na sassan duniya na gaggawar kara shiga kasuwar kasar Sin. To sai dai kuma, kwanaki 2 da suka gabata, sakamakon karin harajin fito da Amurka ta yi, hukumar lura da harkokin fina-finai ta kasar Sin za ta rage adadin fina-finan Amurka da ake shigarwa kasar, matakin da tuni ya haifar da karyewar darajar hannayen jarin manyan kamfanonin shirya fina-finai na Amurka irin su Walt Disney, da Warner Bros da Discovery.
- Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
- Mutane Da Yawa Sun Jikkata Bayan Fashewar Bam A Wata Kasuwa A Ikeja
A lokaci guda, shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta fito fili ta bayyana cewa, Amurka da EU sun gaza cimma daidaito kan batun kare-karen haraji, don haka EU za ta fara hukunta manyan kamfanonin fasaha na Amurka.
Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya.
Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan ci gaba da bude kofarta, da aiki tare da abokan hulda irinsu Sifaniya wajen goyon bayan tsarin cudanyar sassa daban daban, da goyon bayan dunkulewar salon raya tattalin arziki da cinikayya marar shinge, da samar da karin hidimomi, da kayayyaki masu inganci ga kasashen biyu ta hanyar hadin gwiwa da juna, da mutunta juna, da amfanar da al’ummunsu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp