Tun daga shekarar 2018 zuwa watan Oktoban bana, masu gabatar da kara na kasar Sin, sun gurfanar da wadanda ake zargi da amfani da mukaman su ba bisa ka’ida ba sama da 114,000 gaban kuliya, bayan samun amincewar hukumar lura da gabatar da kararraki ta kasar.
Babbar kotun koli ta al’ummar kasar Sin ko SPP ce ta fitar da wadannan alkaluma a kwanan nan, yayin wani taron aiki mai nasaba da yaki da laifuka da ake aikatawa, ta amfani da mukami ba bisa ka’ida ba.
Kaza lika, masu gabatar da kararraki sun shigar da wasu mutanen sama da 16,000 kara, bisa zargin su da bayar da cin hanci, yayin da suke aiwatar da tsare-tsaren kwamitin kolin JKS na dakile karba da bayar da cin hanci, kamar dai yadda zaman taron ya tabbatar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp