Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce ya kamata kasar Japan ta tuna cewa yankin Taiwan bangare ne na kasar Sin, don haka kome zai samu yankin bai shafi kasar Japan ba.
Mao Ning, ta bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin da take amsa tambayar da aka yi mata, yayin taron ‘yan jarida da aka saba gudanarwa, dangane da kalaman baya bayan nan na firaministar Japan Takaichi Sanae kan yankin Taiwan. Mao ta ce Sinawa da dama na ganin a matsayin Japan na kasa dake da nauyin saukewa, dangane da abubuwan da suka faru a tarihin yankin Taiwan, Japan din ba ta cancanci tsoma baki cikin batun Taiwan ba.
A tarihin baya, kasar Japan ta taba amfani da karfi wajen mamaye yankin Taiwan, tare da kakaba tsarin mulkin mallaka na kusan rabin karni, kuma a lokacin, Japanawa ‘yan mamaya sun tafka muggan ayyuka marasa adadi a yankin na Taiwan.
Mao ta kara da cewa, a bana ake cika shekaru 80 da cimma nasarar mayar da Taiwan ga kasar Sin, don haka ya dace Japan ta tuna cewa Taiwan yanki ne na kasar Sin, kuma babu ruwan Japan da duk wani abu da zai samu Taiwan. A daya bangaren kuma, yunkurin amfani da Taiwan don haifar da tashin hankali, ba abun da zai jawowa Japan sai masafi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














