Matakin da Amurka ta dauka na fitar da takardar bayani a kan manufar “Zuba Jari a Amurka ta Zamanto Farko” na matukar kassara hadin gwiwar tattalin arziki da harkokin kasuwanci na yau da kullum a tsakanin kamfanonin Sin da Amurka, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar ciniki ta kasar Sin ya bayyana a jiya Asabar.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce, matakin, wanda ya yi gamin-gambiza da batun tsaron kasa wuri guda, ba komai ba ce illa nuna wariya sannan ya yi hannu riga kwata-kwata da tsarin kasuwanci.
- Thomas Bach: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Bunkasa Wasannin Olympics
- Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata
A cewar jami’in, matakin da Amurka ta dauka na tsaurara matakan tsaro da nufin fakewa da guzuma ta harbi karsana a kan zuba jarin kasar Sin, zai yi matukar illa ga kwarin gwiwar kamfanonin kasar Sin na zuba jari a Amurka.
Har ila yau, mai magana da yawun ma’aikatar ya ce shirin da Amurka ke yi na aiwatar da karin matakan takaita zuba jarinta a kasar Sin dabi’a ce da ba ta dace ba. Kuma da zarar an aiwatar da matakan da ake dauka, za su kara tagayyara hannun jarin kasashen biyu, kuma hakan ba zai yi wa hatta ita kanta Amurkar wani amfani ba.
Jami’in ya kara da cewa, tuni kungiyoyin ‘yan kasuwa da kamfanoni da dama na Amurka suka nuna damuwarsu kan cewa, kakaba takunkumin zuba jari a kasar Sin da Amurka ke yi zai sa kamfanonin kasarta su yi asarar cin gajiyar kasuwar kasar Sin tare da bai wa abokansu na fafatawa damar tsintar dami a kala. (Abdulrazaq Yahuza Jere)