A yau ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na adawa da matakin da Amurka ta dauka, na sanya kamfanonin kasar Sin a cikin sunayen “jerin kamfanoni” da ake kebe na musamman don sanya musu takunkumi, karkashin abin da ake kira wai suna hada baki da kasar Rasha.
A cewarsa, wannan mataki na Amurka bai dace da dokokin kasa da kasa ba, kuma bai samu iznin kwamitin sulhu na MDD ba. Wannan wata al’ada ce ta takunkumi na kashin kai da kuma nuna fin karfi.
Ya kara da cewa, matakin ya yi matukar tauye hakki da muradun kamfanonin kasar Sin, tare da yin barazana ga tsaro da zaman lafiyar masana’antu da samar da kayayyaki a duniya baki daya.
Kakakin ya ce, kamata ya yi kasar Amurka ta gaggauta gyara kura-kuranta, ta kuma daina dakile kamfanonin kasar Sin ba tare da wani dalili ba, yana mai cewa, kasar Sin za ta kare hakki da moriyar kamfanoninta. (Ibrahim)