Kasar Sin ta bayyana matukar rashin jin dadi tare da adawa da matakin Amurka na sanya wasu kamfanonin kasar cikin jerin wadanda ba za a sayarwa kayayyaki ba, da wadanda ba a tantance ba.
Kakakin maaikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ne ya bayyana haka yau Litinin, inda ya ce Sin ta lura da mataki na baya-bayan nan da Amurka ta dauka na kara wasu kamfanoninta 6 cikin jerin wadanda ba za a sayarwa kayayyaki ba da kuma wasu 3 cikin jerin wadanda ba a tantance ba, bisa fakewa da batutuwan da suka shafi ayyukan soji da kuma kasar Iran.
- Haɓaka Tattalin Arziki Ƙasa: Gwamnan Yobe Ya Bai Wa NEPZA Fili Hekta 300
- Gwamna Sani Ya Samu Karramawa Daga Igbo, Ya Bayar Da Fili Don Gina Kasuwar Kayayyakin Gyara
A cewar kakakin, an shafe lokaci mai tsawo, Amurka tana daurin goro game da batun tsaron kasa sannan ta keta matakan takaita fitar da kayayyaki, tare da sanya takunkumai da danne kamfanonin kasashen waje, ciki har da na Sin.
Ya ce ya kamata Amurka ta dakatar da aikata kuskuren nan take, yana cewa, Sin za ta dauki matakan da suka wajaba wajen kare halaltattun hakkoki da muradun kamfanoninta. (Faiza Mustapha)