Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa.
Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda tun daga shekarar 2017, hada-hadar cinikayya ta duniya a fannin rarraba matsakaitan hajoji, ke kara dogaro kan kasar Sin sama da dogaronta ga yankin arewacin Amurka. Kazalika a shekarar 2023, dogaron sassan kasa da kasa kan kasar Sin ta fuskar samar da matsakaitan hajoji ya kai kaso 16 bisa dari, sama da na yankin arewacin Amurka mai kaso 15 bisa dari.
Bugu da kari, rahoton ya ce yamucin cinikayya da Amurka ta haifar a shekarar 2018, bai baiwa Amurkan wata nasara ta fuskar daga matsayinta, a hada-hadar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp