Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali.
Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa. Ya ce Sin ta yi tir da harin ta’addanci da ya auku a yankin Pahalgam, tana kuma adawa da duk wani nau’i na ayyukan ta’adanci.
- 2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC
- 2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC
Wang ya kara da cewa, a yanayin duniya na sauye-sauye da tangal-tangal, samun zaman lafiya da daidaito a yankin Asiya abu ne mai kima da ya wajaba a martaba.
A wani ci gaban kuma, Wang Yi ya zanta ta wayar tarho da mataimakin firaminista, kuma ministan harkokin wajen Pakistan Mohammad Ishaq Dar, inda ya ce a matsayin Pakistan da India na kasashe makwaftanta, Sin ta damu matuka da kara ta’azzarar rikici tsakanin kasashen biyu. Ya ce Sin ta gamsu Pakistan za ta tunkari wannan lamari cikin lumana, da aiwatar da matakai daidai da babban burin cimma moriya mai dorewa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp