Cikin shekaru da dama, kasar na ta aiwatar da matakai daban daban na bunkasa ci gabanta ba tare da lalata yanayi ba, musamman ma bayan da ta kaddamar da shirin hadin gwiwa na BRICS a shekarar 2019, shirin da ke da nufin ingiza hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” ba tare da gurbata yanayi ba.
Ko shakka babu wannan shiri ya zama wani sabon ginshikin samar da ci gaba marar lalata yanayi, wanda zai tabbatar da daukacin bil adama yana gudanar da rayuwa tare da kaucewa fitar da adadin iskar carbon mai dumama yanayi da ta wuce kima. Kuma cimma nasarar hakan zai wakana ne kawai idan dukkanin sassa sun hada karfi da karfe, wajen aiwatar da matakan kare muhalli, da zamanantar da kiyaye muhallin halittu, da cimma burikan dake kunshe cikin ajandar nan ta SDGs, ta ci gaba mai dorewa ta MDD nan zuwa shekarar 2030.
- Sojoji Sun Kama Mutane 20 Kan Zargin Kashe-kashe A Jihar Filato
- Amurka Ta Lahanta Taiwan Na Kasar Sin Ta Hanyar Sayarwa Yankin Da Makamai
Cikin sahihan matakai da kasar Sin ke aiwatarwa domin ganin an cimma nasara, akwai rungumar sabbin makamashi, da rage dogaro kan hanyoyin kona sinadarai dake fitar da iskar carbon fiye da kima.
Alal hakika, Sin ta ciri tuta a fannin nan na samar da ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba, bisa matakan da take aiwatarwa a gida da matakin kasa da kasa. Sin ta samar da sahihan tsare-tsare na cin gajiyar makamashi mai dorewa, da mara baya ga hadin gwiwar dukkanin sassa yayin da ake tunkarar tarin kalubale masu nasaba da sauyin yanayi.
A ganina hadin gwiwar Sin da sauran sassan kasa da kasa zai ci gaba da kasancewa muhimmin jigo, wanda zai ingiza nasarar ajandar nan ta ci gaba mai dorewa, da samar da yanayi mai inganci na kare yanayi, ta yadda daukacin bil adama zai samu damar yin rayuwa mai tsafta, da dakile aukuwar bala’u da samun ci gaba mai dorewa. (Saminu Alhassan)