Muhalli shi ne rayuwa, dukkan halittu na bukatar kyautatuwar muhalli domin samun rayuwa mai inganci da walwala.
A yayin da aka gudanar da bikin ranar muhalli ta kasa da kasa a karshen wannan mako, masu ruwa da tsaki suna ci gaba da jaddada muhimmancin kare muhalli da yin kiraye-kirayen a kaucewa gurbata muhallin halittu, domin samun rayuwa mai inganci gami da kaucewa shiga mawuyacin hali a sakamakon gurbacewar muhallin.
A jawabin da ya gabatar a jajiberin bikin muhalli na shekarar 2022, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce ana bukatar abubuwa masu tarin yawa a wannan duniyar tamu domin tafiyar da rayuwarmu yadda ya kamata, kuma abubuwan dake lalata muhalli ba kawai suna cutar da duniya ba ne, har ma da halittun dake rayuwa cikinta. An yi kiyasin sama da mutane biliyan 3 ne matsalolin tabarbarewar muhallin halittu ya shafa a duniya. Kana gurbacewar muhalli yana sanadiyyar mutuwar wuri na kusan mutane miliyan 9 a duk shekara a duniya, sannan sama da nau’ikan dabbobi da tsarrai miliyan 1 ne ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa a duk shekara a duniya, kamar yadda babban jami’in MDDr ya bayyana. Ya ce nan da shekarar 2050, sama da mutane miliyan 200 ne a duk shekara za su fuskanci barazanar barin muhallansu sakamakon matsalolin sauyin yanayi.
Bisa lura da girman matsalolin da duniya ke fuskanta, ya sa mahukuntan kasar Sin ke tsayawa tsayin daka, wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu na kare muhalli a mataki na cikin gida har ma da matakin kasa da kasa.
Matakan da kasar Sin ke dauka wajen kare muhalli ya yi matukar daukar hankalin kasa da kasa, kamar yadda Elizabeth Maruma Mrema, babbar sakatariyar sashen kula da nau’ikan halittu ta MDD ta ce, kasar Sin ta cimma muhimman sakamako masu karfafa gwiwa a fannonin yaki da matsalar sauyin yanayi, da kandagarkin bacewar nau’in halittu, da rage iska mai gurbata muhalli. Mrema ta yi wannan tsokaci ne a lokacin bikin ranar kare muhalli ta kasar Sin ta shekarar 2022, inda ta bayyana hakan a jawabin da ta gabatar. Taken bikin na bana shi ne, “mu yi aiki tare don gina kyakkyawar duniya mai tsafta.” Jami’ar MDD ta ce, kasar Sin ta yi aiki tukuru, tare da bayar da gagarumar gudunmawa ga kokarin da duniya ke yi wajen magance matsalolin dake shafar muhalli, da daga matsayin aikin gina cigaba mai dorewa, da kuma gina makomar al’umma don kyautata rayuwar dukkan bil adama a duniya. Bugu da kari, ta kuma yabawa matakan da kasar Sin ke dauka wajen kiyaye nau’ikan halittu, matakan da suka hada da kafa lambunan shan iska na kasa, da kuma samar da dokokin dake shafar kiyaye muhallin halittu. Guterres ya bukaci gwamnatoci da su bada fifiko wajen daukar matakan tinkarar matsalolin sauyin yanayi, da kare muhalli, ta hanyar bullo da manufofin da zasu taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Cikin wasikar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike don taya murna bikin ranar muhalli ta kasar Sin na shekarar 2022, ya yi nuni da cewa, muhallin halittu shi ne ginshikin rayuwa da ci gaban dan Adam, kuma kiyaye muhalli yadda ya kamata shi ne burin bai daya na jama’ar kasashe daban daban. Ya ce tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kasar Sin ta dauki aikin raya al’adun halittu a matsayin wani muhimmin shiri mai alaka da samun dauwamammen ci gaban al’ummar kasar, tana kuma tsayawa kan ra’ayinta na “tabbatar da kyakkyawan muhalli shi ne arzikinmu”.
Ranar muhalli ta duniya, ta kasance a matsayin wani muhimmin lokaci da MDD ke amfani da shi, wajen fadakar da duniya game da matakan da suka dace a dauka don kare muhalli. (Ahmad Fagam)