Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024, a matsayin hutu domin bikin Maulidin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya sanar da wannan a madadin gwamnati cikin wata sanarwa daga Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dokta Magdalene Ajani ta fitar.
- Sin Na Shirin Soke Daukacin Haraji Kan Hajojin Dake Shiga Kasar Daga Kasashe Mafiya Karancin Wadata
- GORON JUMA’A
Ya taya Musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya murna wannan lokaci mai muhimmanci.
Ministan ya yi kira ga Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin samun zaman lafiya mai dorewa da ci gaban kasa.
Haka kuma, ya roki ‘yan Nijeriya da su rungumi halin hakuri, sadaukarwa, da juriya a wannan lokaci.