Ran 30 ga watan nan da muke ciki, kasar Sin ta cimma nasarar harba kumbon Shenzhou-16. Kafin an harba kumbon, mai magana da yawun hukuma mai kula da harkokin nazarin sararin samaniya ta kasar Sin ya bayyana cewa, Sin na maraba da ‘yan saman jannati na sauran kasashe da su yi amfani da tasharta ta samaniya, don hadin kai wajen gudanar da ayyukan nazari, da more ci gaba tare.
Aiwatar da hadin gwiwa a fannin nazarin harkokin samaniya, bukatun bai daya ne na kasashe daban-daban, kuma Sin na nacewa ga yin mu’ammala da hadin kai da sauran kasashe, ko hukumomin nazarin sararin samaniya, da kungiyoyin kasa da kasa a wannan fanni.
A nahiyar Afirka kuwa, hadin kan bangarorin biyu ya zama karfin ingiza hadin kansu, karkashin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Bangarorin biyu sun yi hadin kai a fannin fitar da tauraron dan Adama da aka harhada, da gina manyan ababen nazarin sararin samaniya, da nazarin tauraron dan Adam, tare da cimma nasarori da dama. Ci gaban kimiyya da fasaha a wannan fanni, suna kara karfin zamanintar da rayuwar al’umma da tattalin arzikin Afrika.
Dan saman janati na farko da ya taka doron duniyar wata Neil Alden Armstrong, ya taba bayyana cewa, dan karamin matakin da ya yi a doron duniyar wata, babban ci gaba ne ga dan Adam baki daya.
Nasarorin da Sin take samu a fannin nazarin sararin samaniya, ba ma kawai ci gaban da take da shi ba ne, haka kuma ci gaba na bai daya ne ga daukacin Bil Adama. Sin na nacewa ga nazarin sararin samaniya cikin lumana, ta hadin kai da sauran sassan kasa da kasa, ta yadda daukacin bil Adama za su more wannan ci gaba. (Mai zana da rubuta: MINA)