Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Talata cewa, game da harin da wasu ‘yan ta’adda suka kaddamar a Pakistan, Sin na matukar bakin ciki, tare da sukar lamarin da kakkausar murya, kuma Sin na tsayawa tsayin daka kan yaki da ta’addanci.
A cewarta, Sin za ta nace ga nuna adawa ga matakin da Amurka ke dauka, na amfani da karfin iko yadda take so, a fannin dakile kamfanoni masu jarin Sin, ta hanyar fakewa da batun tsaron kasar.
Game da wasu manufofin shigar Sinawa wasu kasashe kuwa, Mao Ning ta ce, Sin ba ta amince da matakan sanyawa Sinawa takunkumin shiga kasashen ba, kuma matakin nuna bambanci ne.
Ban da wannan kuma, game da batun yadda wasu kasashe suka hana fitar da sassan da ake hada kayan laturoni da su zuwa kasar Sin, Mao Ning ta ce fatan shi ne wadannan kasashe za su rungumi matsayar adalci, da daidaito, don yanke shawarar dogaro da karfin su. (Amina Xu)