Rahotanni daga hukumar raya hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin na cewa, a Asabar da ta gabata ne wani rukunin kayayyakin jinya da darajarsu ta kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.39 ya tashi daga birnin Shanghai na kasar Sin, a wani bangare na tallafin jin kai da kasar Sin ta samar ga kasar Sudan.
Tun bayan barkewar rikici a kasar Sudan, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali matuka, kan halin jin kai da ake ciki a kasar, tare da yanke shawarar kai agajin gaggawa ga kasar. Kayayyakin sun kunshi tan 939 na shinkafa da kayan aikin kiwon lafiya kamar safar hannu na gwaji, da bandeji, da riguna da hulunan tiyata. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp