Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce Sin na matukar adawa da aniyar Amurka ta dora karin haraji kan wasu hajojin Sin dake shiga kasar, ta kuma gabatar da korafi game da hakan.
A baya-bayan nan ne dai ofishin wakiliyar cinikayyar kasar Amurka ko USTR, ya sanar da batun karin harajin, karkashin sashe na 301, na dokar cinikayyar Amurka ta shekarar 1974, kan hajojin Sin dake shiga Amurka, da suka hada da ma’adanin tungsten, da wafers da polysilicon.
- Ba Zancen Karɓa-Karɓa A Shugabancin Nijeriya, Na Gari Ake Buƙata – Shekarau
- Kungiyoyin Sa-ido Na Kasa-da-kasa Sun Yaba Da Zaben Ghana
Wata sanarwar da ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar a Litinin din nan, ta ce Sin za ta aiwatar da karfafan matakai na kare hakkoki da moriyarta. Kaza lika, tuni kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ta bayyana amfani da wancan sashe na 301, wajen kakaba karin haraji a matsayin abun da ya sabawa dokokin kungiyar.
Matakin karin haraji da Amurka ke dauka ba zai warware gibin cinikayya ba, kuma hakan zai illata moriyar Amurkawa masu sayayya, da haifar da hargitsi a tsarin gudanar tattalin arzikin duniya, da tsaro da daidaiton tsarin samarwa, da rarraba hajoji tsakanin sassan kasa da kasa.
Don haka bangaren Sin ke kira ga Amurka, da ta gaggauta gyara kuskurenta, ta kawar da wannan batu na karin haraji kan hajojin kasar Sin. (Saminu Alhassan)