Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bayyana Alhamis din nan cewa, har kullum kasar Sin tana fatali da yadda ake siyasantar da kuma amfani da cinikayya a matsayin wani makami, kuma ta himmatu wajen kiyaye tsarin yin ciniki cikin sauki da ‘yanci a duniya.
Mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana hakan, yayin da take mayar da martani kan ikirarin da sakatariyar baitul malim Amurka Janet Yellen ta yi cewa, tilas ne Amurka ta kiyaye amfani da cinikayya a matsayin sanya duniya cikin rigima, da kasashe ke yi, wai ciki har da kasar Sin. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)