Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce kasarsa ta yi takaicin yadda kwamitin tsaron MDD ya gaza zartas da kudurin tsaron sararin samaniya da aka gabatar gabansa a watan da ya gabata.
Fu Cong ya ce, bayan gaza zartas da kudurin na watan Afirilu wanda kasashen Amurka da Japan suka gabatar, kasar Rasha ta sake gabatar da wani sabon kuduri mai nasaba da batun, wanda ke kunshe da muhimmanci, da gudummawar da yarjejeniyar kare sararin samaniya ke da shi, tare da tallafinta wajen fayyace haramcin jibge duk wasu nau’in makamai a sararin samaniya, da kuma kira game da gaggauta kammala yarjejeniyar dakile shigar makamai sararin samaniya.
- Xi Ya Taya Zababben Shugaban Chadi Mahamat Deby Murna
- Ƴansanda Sun Dakile Hari, Sun Ceto Mutane A Abuja
Sassan kudurin dai sun samu karbuwa matuka daga sama da kaso biyu bisa uku na mambobin babban taron MDD, duba da yadda suka kunshi damuwa da muryoyin sassan kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa.
Fu ya ce, Sin na goyon baya, ta kuma hada gwiwa da Rasha wajen gabatar da kudurin da Rashan ta gabatar. To sai dai kuma abun takaice, sakamakon sabanin matsayar wasu sassa, ya haifar da kin amincewa da kudurin, lamarin da Sin din ta bayyana a matsayin mai bakanta rai. (Saminu Alhassan)