Kamfanin kirar jiragen sama na kasar Sin wato AVIC ya ce ya cimma nasarar samar da jirgin sama dake iya tashi a kasa da ruwa irinsa na farko samfuri AG600 da aka yiwa lakabi da “Kun Long”. An kuma cimma nasarar gwajinsa a jiya Lahadi a birnin Zhuhai na lardin Guangdong.
Hakan ya nuna cewa, ingancin jirgin ya dace da ma’aunin da aka tanada, kuma ya alamta cewa jirgin samfuri AG600 ya samu iznin kira wato PC.
Rahotanni na cewa a ranar 20 ga watan Afrilun bana, jirgin samfurin AG600 ya samu takardar shaidar inganci ta samfurinsa, matakin da ya nuna cewa, nazarin da aka yi a wannan bangare ya cimma cikakkiyar nasara, kuma jirgin ya samu izinin shiga kasuwa. Kazalika, kamfanin AVIC zai gaggauta tabbatar da cewa “Kun Long”, ya taka rawa a fannin ba da agajin gaggawa, da tinkarar da kuma kandagarkin bala’u daga indallahi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp