Da karfe 7 saura mintuna 9 na safiyar yau Laraba ne kasar Sin ta cimma nasarar harbar tauraro na 2 na Yunhai-3, daga cibiyar harba kumbo ta Taiyuan, ta amfani da rokar “Changzheng-6 ko (CZ-6)”, wato Long March 6 da aka kai cibiyar dauke da kayayyakin harba tauraron. Daga baya, tauraro ya kama hanyarsa zuwa sararin samaniya yadda aka tsara.
Muhimmin aikin tauraron na 2 na Yunhai-3 shi ne binciken yanayin teku, da na sararin samaniya, domin kandagarkin bala’u daga indallahi, da gudanar da gwaje-gwajen kimiyya da dai sauransu.
Aikin na wannan karo shi ne karo na 514 da aka yi amfani da rokar CZ-6 wajen harba kumbuna. (Amina Xu)