Mahukunta a kasar Sin sun fara samar da tallafin kudade domin karfafa gwiwar masu sayayya dake bukatar sauya kayayyakin da suke amfani da su a gidaje da sababbi, kamar dai yadda wata sanarwa da ma’aikatar cinikayya da wasu sassan gwamnati 3 suka fitar ta nuna.
Kayayyakin da al’umma za su samu tallafin yayin sayensu, sun kunshi wadanda ke karkashin rukunoni 8, dake aiki da mafi ingancin makamashi, ciki har da firji, da injin wanki, da talabijin, da na’urar sanyaya daki, da na’urori masu kwakwalwa. Rangwamen dai zai kai na kaso 15 bisa dari na jimillar kudin sabbin kayayyakin da ake bukatar saya.
- Fina-finai Masu Dogon Zango Koma Baya Ne Ga Masana’antar Kannywood – Tanimu Akawu
- NYSC Ta Mayar Da Sansaninta Na Bauchi Zuwa Kwalejin Kangere
Sanarwar da aka fitar, ta ce an umarci kananan hukumomi da su tsara shirin amfani da kudade daga gwamnatin tsakiya, da na kananan yankuna, domin samar da tallafin rangwamen ga masu sayayya, wadanda ke burin sayen kayayyaki daga wadannan rukunoni 8.
A watan Maris ne majalissar gudanarwar kasar Sin ta fitar da babban shirin daga matsayin nagartar kayayyakin da al’ummar kasar ke amfani da su, da sauya nau’o’in kayayyakin amfani a gidaje ta hanyar musaya da sababbi.
Ya zuwa karshen shekarar 2023, al’ummun kasar Sin sun mallaki ababen hawa miliyan 336, da manyan kayayyakin amfani a gidaje sama da biliyan 3. Ana kuma fatan daga matsayin ingancin kayayyakin amfani a gidaje a kasar zai samar da bukatun kasuwa da darajar su za ta kai sama da yuan tiriliyan daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)