Sin ta kammala amfani da tauraron dan adam wajen sa ido kan manyan hanyoyin wutar lantarki jiya Alhamis a lardin Jiangsu, wanda ya kara ingancin aikin kula da wutar lantarki da rage haddura.
A wannan zagaye na sa ido, an yi amfani da tsarin gano matsaloli ta tauraron dan adam wanda Sin ta samar da kanta, inda aka gudanar da binciken matsaloli a kan hanyoyin wutar lantarki fiye da 270 dake dauke da kilovolt 500 ko sama da haka. Nisan hanyoyin da aka sa wa ido ya wuce kilomita 15,000, kuma ingancin aikin ya ninka aikin dan adam sau 10.
A yanzu haka, tsawon hanyoyin wutar lantarki na kilovolt 500 ko sama da haka a Sin ya kai fiye da kilomita 320,000. Saboda haka, Sin tana kokarin binciko hanyar amfani da fasahar hangen nesa ta tauraron dan adam don magance matsalolin rashin ingancin sa ido daga aikin dan adam da kuma iyakokin da ke tattare da amfani da jiragen sama marasa matuka.(Safiyah Ma)