Kasar Sin ta fitar da wani sabon shiri na shekaru 3, domin kyautata yanayin kasuwanci a yankin Guangdong-Hong Kong-Macao na kasar, ta yadda yankin wanda a kan kira da “Guangdong, Hong Kong, Macao Greater Bay Area” a Turance, zai zamo kan gaba a duniya ta fuskar kasuwanci.
An fitar da shirin ne a jiya Litinin, kuma a cewar wata majiya daga hukumar tsara manufofin samar da ci gaba, da aiwatar da sauye sauye ta kasar Sin, ana fatan hakan zai zurfafa hadin gwiwar sassan yankunan, da inganta dunkulewar kasuwanni, da raya takarar cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa a yankin.
Tsarin da aka tanada domin cimma wannan buri, ya nuna yadda za a kafa manufofi, da tsare tsaren ayyuka masu nasaba, wadanda za su dace da dokokin kasa da kasa, da za su ingiza karsashin kasuwanni, da kirkire-kirkire, tare da baiwa yankin damar kara janyo jari daga dukkanin sassan duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp