• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Abun Da Zai Biyo Bayan Ziyarar Nancy Pelosi A Yankin Taiwan

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce gwamnatin kasar Sin na jan kunnen Amurka, da ta dakatar da shirin da kakakin majalissar wakilanta Nancy Pelosi ke yi, na ziyartar yankin Taiwan na kasar Sin.

Kuma idan har Pelosi ta gudanar da wannan ziyara, kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi, kuma Amurka ce za ta dauki alhakin duk abun da ya biyo baya.

  • Wani Dan Kasuwan Kasar Sin Ya Bullo Da Shirin Magance Matsalar Gurbataccen Ruwa Sha A Nahiyar Afirka

Zhao ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na Talatar nan, yana mai cewa, bangaren Sin ya sha nanata rashin amincewa, da duk wani nau’in ziyara da jami’an Amurka za su kai yankin na Taiwan, kuma yin hakan zai sanya Sin aiwatar da matakai masu karfi, na kare ikon ta na mulkin kai, da tsaron yankunan ta.

Ya ce majalissar dokokin bangare ne na gwamnatin Amurka, don haka duk wani jami’in majalissar ya wajaba, ya martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Jaridar Financial Times ta rawaito cewa, Pelosi na shirin ziyartar yankin Taiwan cikin watan Agusta mai zuwa, ko da yake jaridar ta ce akwai rabuwar kawuna tsakanin jami’an gwamnatin Amurka, game da yiwuwar gudanar da ziyarar.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

Kafin hakan, mahukuntan Sin sun nuna matukar rashin amincewa, tare da gabatar da korafi ga bangaren Amurka, don gane da ziyarar da Pelosi ta shirya kaiwa yankin na Taiwan a watan Afirilun da ya shude, inda daga bisani jami’ar ta ce ta dage ziyarar, saboda harbuwa da ta yi da cutar COVID-19. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Next Post
Buhari Ya Bai Wa Ministan Ilimi Mako 2 Don Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.