Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 na kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kai, a babban zauren taron jama’a na Xinjiang. Kuma shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bikin.
Memba dindindin na ofishin siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kana shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ko CPPCC, kuma shugaban tawagar kwamitin kolin jam’iyyar Wang Huning, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. Kazalika, memba dindindin na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Cai Qi shi ma ya halarci taron.
A cikin jawabinsa, Wang Huning ya bayyana cewa, kwamitin kolin JKS a karkashin jagorancin Xi Jinping, ya ci gaba da dubawa, da tsai da tsare-tsaren gudanar da harkokin Xinjiang daga mahangar dabarun siyasa na zamani, ta yadda za a ingiza ci gaban wuri a mabambantan bangarori, tare da cimma nasarar kawar da kangin talauci tare da al’umomin yankin. Kana da gina al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni, da zurfafa hadin kan al’ummar Xinjiang, ta yadda jama’a za su kasance tare kamar ’ya’yan rumman, su yi tafiya bai daya a kan hanyar ci gaban Sin.
Wang Huning ya kara da cewa, Xinjiang na kan wani sabon mataki na tarihi na samun ci gaba. Don haka dole ne a ci gaba da bin salon jagorancin Xi Jinping bisa ruhin tsarin gurguzu mai sigar musamman a sabon zamani, kuma a aiwatar da tsarin gudanar da harkokin Xinjiang da JKS ta tsara yadda ya kamata. Har ila yau, a nace da kyautata tsarin cin gashin kai a yankin. Kana ya bukaci a yi kokari don gina Xinjiang mai hadin kai, da zaman lafiya, da wadata, da ci gaban al’adu da kuma muhalli mai kyau. (Amina Xu)














