Da karfe 10:03 na safiyar yau Asabar ne kasar Sin ta yi nasarar harba kumbon dakon kayayyaki mai suna Tianzhou-5, wajen aikewa da kayayyaki zuwa tashar sararin samaniya ta kasar, wadda ake fatan kammalar ta zuwa karshen shekarar nan.
Hukumar lura da ayyukan saman jannati ta kasar Sin ko CMSA, ta ce an harba kumbon ne ta amfani da rokar Long March-7 Y6, daga cibiyar harba taurarin dan adam ta Wenchang, dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin.
CMSA ta ce bayan mintuna 10 da harba kumbon, Tianzhou-5 ya rabu da rokar Long March-7 Y6, ya kuma shiga falakin sa cikin nasara. Ba da jimawa ba, faifan makamashin hasken rana dake jikin kumbon ya bude, tare da fara aiki yadda ya kamata. CMSA ta ce an kammala aikin harba kumbon cikin nasara.
Daga baya, kumbon ya hade da tashar samaniya ta Tiangong. Wannan ne karon farko da ‘yan sama jannati da ke cikin tashar binciken samaniya da Sin ke ginawa suka ga isar kumbon dakon kayayyaki. (Saminu Alhassan)