ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Jadadda Wajibcin Daukar Jerin Matakan Magance Matsalar Talauci Da Karancin Ci Gaba Da Rikici

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Sin

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong, ya gabatar da jawabi a gun taron muhawara mai taken “Talauci da karancin ci gaba da rikici”, wadda kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a jiya Alhamis, inda ya ce matsalar fama da talauci, da rashin samun ci gaba, muhimman dalilai ne dake haifar da rikice-rikice, don haka ya kamata a yi hangen nesa, da tabbatar da shirin magance su baki daya.

Fu ya ce, “Dole ne mu taimakawa kasashe masu tasowa, ta yadda za su samu ci gaba, da mutunta hanyoyin da suka zaba na bunkasa bisa karfin kashin kansu, kana da zurfafa huldar abota ta hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kuma ingiza kyautata tsarin daidaita harkokin duniya, da baiwa aikin wanzar da zaman lafiya a duniya muhimmanci.”

  • Ba Tsoro Ne Yasa Muka Amince Da Sulhu Da Ƴan Bindiga Ba – Gwamnatin Sokoto
  • Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma

Jami’in ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su gaggauta baiwa batun samun ci gaba muhimmancin gaske cikin ajandar kasa da kasa, ta yadda za a sanya batun rage talauci, da ba da ilmi, da tabbatar da samar da guraben aikin yi, da habaka karfin samun ci gaba da sauransu gaban komai, da kuma tabbatar da ba a bar kowa a baya ba.

ADVERTISEMENT

Fu Cong ya kara da cewa, Sin ta gabatar da shawarar tsaron kasa da kasa, inda ta yi kira ga bangarori daban-daban na duniya, da su nacewa ra’ayin tsaro dake bukatar yin hadin gwiwa a dukkanin fannoni masu dorewa, matakin da ya gabatar da shiri iri na kasar Sin, ta fuskar warware rikice-rikice mafiya jawo hankali a siyasance.

Ya ce Sin tana iyakacin kokarinta, wajen shiga a dama da ita a sha’anin raya kasashen duniya baki daya, kuma tana hadin gwiwa da sauran kasashe, don tabbatar da nasarar ingantacciyar shawarar “ziri daya da hanya daya”, wanda hakan zai gaggauta ci gaban sassan kasa da kasa baki daya.

LABARAI MASU NASABA

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Kazalika, a cewar jami’in, Sin na kara bude kofarta ga ketare bisa matsayin koli, da shigo da jari cikin kasar a bangaren sana’o’in samar da kayayyaki, kana da yafe dukkannin harajin kwastam ga kasashen Afirka mafiya fama da karancin ci gaba da suka kulla dangantakar diplomasiyya da ita. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Next Post
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025
ECOWAS

A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS

November 16, 2025
APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

November 16, 2025
Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.