Yau da safe, an yi gaggarumin bikin ba da lambobin yabo da karramawa na kasar Sin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar kuma shugaban kwamitin soja na kasar Sin Xi Jinping ya ba da lambobin yabo da karramawa na kasar Sin ga jaruman kasar, tare da gabatar da jawabi.
Xi ya nuna cewa, Sin ta samu gaggarumin ci gaba a bangaren samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da raya kwanciyar hankalin al’umma mai dorewa a cikin shekaru 75 da suka gabata tun kafuwar sabuwar kasar Sin, karkashin kokarin al’ummar Sinawa a duk fadin kasar bisa jagorancin JKS, jarumai da dama sun ba da gudunmawarsu, kuma wadanda suka samu lambobin yabo a yau su ne fitattun wakilai daga cikinsu. Kasar ba za ta manta da labarai da gudunmawar da suka bayar ba, dole ne al’ummar Sinawa su yi koyi da ruhinsu na neman cika buri da karfin zuciya da halayen jajircewa.
Xi ya kara da cewa, a cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, abokai da dama suna bin hanya iri daya tare da Sin, sun goyi bayan juna da magance wahalhalu tare, Madam Dilma Rousseff ta kasance daya daga cikinsu, shi ya sa Sin ta ba ta lambar yabo ta sada zumunci. Sin ba za ta manta da abokai baki wadanda suke ba da gudunmawa ga bunkasuwar Sin da damar kara dankon zumunci tsakanin al’ummar Sin da sauran kasashe ba. Sinawa na fatan hadin gwiwa da al’ummomin kasa da kasa don kiyaye zaman lafiya da gaggauta samun bunkasuwa tare da kafa wata kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, wanda zai kai ga kafa wata makomar mai haske ga bil Adama nan gaba. (Amina Xu)