A yau Talata ne kasar Sin ta kaddamar da tsarin samar da tallafin gaggawa ga kasashen Türkiyya da Syria, bayan mummunar girgizar kasa da ta aukawa wasu yankunan kasashen 2.
Da yake bayyana hakan, mataimakin shugaban hukumar kula da hadin gwiwar kasa da kasa kan harkokin ci gaba ta kasar Sin Deng Boqing, ya ce Sin za ta samar da tallafin jin kai na farko da darajarsa za ta kai yuan miliyan 40, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 5.89 ga kasar Turkiyya.
Deng ya kara da cewa, Sin tana kuma tsara wani shiri na samar da kayan tallafin jin kai ga Syria, da hanzarta aiwatar da tallafin samar da abinci, domin wadanda ibtila’in ya aukawa.
Kazalika da yammacin yau, gwamnatin Sin ta aike da jami’an aikin ceto 82, tare da kayan aiki da ake bukata, domin su ba da gudummawa ga sassauta halin matsi, ga wadanda girgizar kasar ta rutsa da su a Türkiyya.
A wani ci gaban kuma, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce kasar ta ta damu matuka game da aukuwar girgizar kasar mai tsanani a Türkiyya da Syria, kuma za ta yi iyakacin kokarin taimakawa kasashen 2.
A yau Talata, mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fuat Oktay, ya sanar da cewa, adadin mutane da suka rasu sakamakon aukuwar girgizar kasar a yankin kudu maso gabashin kasar ya karu zuwa mutum 3,419, adadin da in an hada da wadanda suka rasu a Syria, ya kai sama da mutum 5,000. (Saminu Alhassan)