A yayin da yake halartar taron koli karo na 20 na kungiyar G20 da ya gundana a makon da ya wuce, firaministan kasar Sin Li Qiang ya sanar da cewa, kasarsa da Afirka ta kudu ne suka gabatar da shawarar hadin gwiwa ta goyon bayan zamanantar da nahiyar Afrika, lamarin da ya jawo hankulan sassa daban daban. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya yi tsokaci kan batun a yayin taron manema labaru da aka saba yi na yau Alhamis cewa, kasar Sin ta kasance aminiya kuma mai bayar da goyon baya mai karfi ga Afirka a fannin zamanantar da kasashen nahiyar, kuma kasar ta yi kira ga dukkan kasashen Afirka da muhimman abokai na neman ci gaba, su sa himma wajen goyon baya da aiwatar da shawarar, don ba da gudunmowarsu kan tabbatar da zamanantar da kasashen tun da wuri.
Kakakin ya kuma bayyana cewa, kaddamar da shawarar hadin gwiwa ta goyon bayan zamanantar da nahiyar Afrika, muhimmin ra’ayin bai daya ne da shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Afirka ta kudu Matamela Cyril Ramaphosa suka cimma a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a watan Satumba na shekarar 2024. Kana firaminista Li ya sanar da gabatar da shawarar bisa hadin kan kasashen biyu a yayin taron koli na G20. Game da haka, kasashen duniya na ganin cewa, shawarar ta nuna rawar jagoranci da kasar Sin ke takawa wajen goyon bayan ayyukan zamanantar da kasashen Afirka, za kuma a kara karfin kasashen Afirka na neman ci gaba da kansu, da kuma kara azama ga ci gaba da farfadowar kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)














