Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta nuna adawa da yadda Amurka ta sanya kamfanoni da daidaikun jama’ar kasar Sin fiye da 24, a cikin jerin sunayen sassan da aka haramtawa kamfanonin kasar Amurka su yi ciniki da su, tana mai kira ga Amurka da ta daina cin zalin kamfanonin kasar Sin ba tare da wani dalili ba.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labarai na Jumma’ar nan cewa, Sin na kira ga Amurka da ta mutunta gaskiya, tare da yin watsi da akidar nuna kyama, da samar da yanayi na adalci kuma ba tare da rufa-rufa ba, da rashin nuna wariya ga kamfanonin kasashen waje dake Amurka.
Ta kara da cewa, bangaren kasar Sin zai dauki matakan da suka dace, don kiyaye halastattun hakkokin kamfanoninta. (Ibrahim)