Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Jumma’a cewa, kasarsa ta sake bukatar Amurka, da ta yi bayani filla-filla kan yadda ita kanta take girmama yarjejeniyar haramta makamai masu guba, maimakon kasar Ukraine, ta kuma daina yin adawa da kafa tsarin binciken yarjejeniyar haramta makamai masu guba.
Rahotanni sun nuna cewa, ma’aikatar tsaron Amurka ta bullo da wasu abubuwa, inda ta jaddada yadda kasar Ukraine take girmama yarjejeniyar, amma ba ta yi bayani sosai ba kan yadda ita kanta take wannan aiki.
Zhao Lijian ya jaddada cewa, Amurka ta fi sauran kasashen duniya tafiyar da ayyukan soja ta hanyar amfani da makamai masu guba, kuma ita ce kasa daya tilo da ta nuna adawa ga kafa tsarin binciken yarjejeniyar haramta makamai masu guba. Kasashen duniya sun nuna damuwa sosai kan irin wannan batu.
Kwanan nan kasar Rasha ta fayyace yadda Amurka ta gudanar da ayyukan soja ta hanyar amfani da makamai masu guba a Ukraine, kuma ta zargi Amurka da sabawa yarjejeniyar, wadda ta ayyana cewa, ya dace Amurka ta yi bayani dalla-dalla kan wannan batu, a wani matakin da zai sanya kasashen duniya su sake nuna imani kan Amurka. (Murtala Zhang)