Kasar Sin ta samar da kudade har yuan biliyan 6.66, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 926.5, domin gudanar da ayyukan farfado da kauyuka, na yankuna masu tarin kananan kabilu a kasar.
Da yake tabbatar da hakan, daraktan hukumar lura da harkokin kabilun kasar Sin Pan Yue, ya ce za a yi amfani da kudaden wajen tallafawa yankunan, a fannonin fadada nasarorin da suka cimma na rage talauci, da kara ingiza farfadowar yankunan karkara. (Saminu Alhassan)