Kasar Sin ta fito da wasu matakai, da nufin bunkasa yadda za a rika zakulo da kula da matasa masu hazaka a fannin kimiyya da fasaha, a wani mataki na saukaka burin kasar na zama mai karfi a fannin kimiyya da fasaha.
Kundin wanda babban ofishin kwamitin kolin JKS da na majalisar gudanarwar kasar suka fitar, ya bukaci da a zage damtse wajen goyon bayan da yiwa matasa masu hazaka jagora, ta yadda za a samu ci gaba mai inganci, da karfafa musu gwiwar gudanar da ayyukan kirkire-kirkire, da cimma nasarori, da amfani da sakamakon binciken da aka gudanar a zahiri.
A cewar kundin, ya kamata a baiwa matasa masu hazaka a fannin kimiyya da fasaha wata dama a manyan ayyukan kimiyya da fasaha, da muhimman sassan binciken fasaha, da bincken kimiyya da fasaha na gaggawa. (Ibrahim)