Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta shaidawa taron manema labarai na yau da kullum Alhamis din nan cewa, kasar Sin tana maraba da kuma nuna godiya ga kokarin kasashen Saudiyya da Iran na kyautata alakar dake tsakanin kasashen biyu, kana a shirye take ta ba da gudummawar hikima da ikonta, don inganta tsaro, da kwanciyar hankali da ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya.
Tun da farko a yau din ne kasashen Saudiyya da Iran, suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu a nan birnin Beijing. Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya shaida bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp