A yau ne, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru cewa, Sin tana bin manufar kare hakkin dan Adam da ta mayar da jama’a a gaban kome, tana mai jaddada cewa, rayuwar jin dadin jama’a, ita ce mafi girman hakkin dan Adam. Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga raya da kare hakkin dan Adam don yada darajar dukkan dan Adam.
Game da rahoton shekara-shekara kan hakkin dan Adam na jihar Xinjiang da ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar da saka takunkumi ga jami’ai biyu na kasar Sin, Mao Ning ta ce, Amurka ta sake yada jita-jita game da jihar ta Xinjiang, da sakawa kamfanonin Sin da ma’aikatansu takunkumi ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam na jihar Xinjiang, lamarin da ya yi mummunar illa ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma Sin tana adawa da kakkausar murya kan hakkoki da muradun kamfanoni da daidaikun mutane.
Haka zalika, game da yadda Amurka ta ki amincewa da kudurin kwamitin sulhu na MDD game da tsagaita bude wuta a zirin Gaza nan da nan, Mao Ning ta ce, ko da yake kudurin bai samu amincewa ba, amma bai kamata kasa da kasa su daina sa kaimi ga neman tsagaita bude wuta da tabbatar da tsaron fararen hula da sassauta rikicin jin kai a zirin Gaza ba. Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da kasa da kasa don cimma burin tsagaita bude wuta a zirin Gaza. (Zainab)