A yau ranar 27 ga wannan wata ne, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru cewa, an bude bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya na kasar Sin karo na biyu a birnin Beijing, inda aka samu halartar kamfanoni kimanin 700 daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 69, an kuma samu halartar kashi 60 cikin dari daga cikin kamfanoni 500 da suke kan gaba a duniya da manyan kamfanoni a sana’o’i daban daban, kana yawan kamfanonin waje ya karu zuwa kashi 32 cikin dari bisa kashi 26 cikin dari na karon da ya gabata.
A cikin dogon lokaci, kasar Sin ta yi kokarin shiga aikin samar da kayayyaki a duniya, kana ta tabbatar da kuma raya tsarin a wannan fanni, wadda ta samar da gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. A halin yanzu, an rasa karfin bunkasa tattalin arzikin duniya, wasu ayyuka masu bin ra’ayin ba da kariya ga cinikayya da kiyaye tsaro sun kawo illa ga aikin samar da kayayyaki a duniya, ta hakan za a kara yawan kudin kashewa na kamfanoni, da hana samun bunkasuwa tare. Kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da samar da kayayyaki a duniya, da yin kokari tare da kasa da kasa wajen sa kaimi ga gina tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa. (Zainab Zhang)