Taron ayyukan raya tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, na shekarar 2025, ya sanya “ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da inganta hadin gwiwa a fannoni da dama”, a matsayin daya daga cikin muhimman ayyukan raya tattalin arziki na kasar Sin a shekara mai zuwa, sannan ya tsara mataki na musamman, na “fadada bude kofa a fannin ba da hidima”.
Fadada bude kofa a fannin ba da hidima, muhimmin sashi ne na bude kofa ga kasashen waje, kuma muhimmin goyon baya ne ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
Mataimakiyar mai nazarin ilmin tattalin arzikin waje, na cibiyar nazarin ci gaba a majalisar gudanarwa ta kasar Sin Chen Hongna, ta bayyana cewa, a cikin wannan yanayi, mayar da “fadada bude kofa a fannin ba da hidima” cikin muhimman matakan bude kofa ga kasashen waje, mataki ne da ya shaida niyyar kasar Sin ta fadada bude kofarta, yana kuma nuna muhimmiyar alamar bullo da sabbin hanyoyin ci gaban tattalin arzikin kasar ta dogaro da ba da hidima. (Amina Xu)














