Gamayyar kungiyar mata ta kasar Sin, za ta kaddamar da jerin wasu shirye-shirye a bana, da nufin karfafa gwiwar mata, ta yadda za su iya sauke nauyin dake wuyansu, ta fuskar ingiza nasarar ci gaba mai nagarta. A cewar kungiyar, za a kafa dandaloli na kasa da kasa da na cikin gida, wadanda za su zaburar da kirkire-kirkiren fasahohi, wanda hakan zai tallafi mata masu ayyyuka a fannin fasaha, wajen samun damar ingiza ci gaba a masana’antun kirkire-kirkire ta hanyar ci gaban fasahohi.
Har ila yau, kasar Sin za ta samar da tsare-tsaren cin gajiya daga gudummawar matan dake yankunan karkara, ciki har da karfafa gwiwar gina dandaloli sama da miliyan 10, a garuruwa daban daban dake sassan kasar, da renon mata jagorori a fannin samar da wadata.
Kaza lika, za a aiwatar da hadin gwiwa da sauran sassa, don kaddamar da gangamin yayata samar da guraben ayyuka, da fadada damammakin samar da ayyuka da sana’o’i ga mata. (Saminu Alhassan)