Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya kai ziyara a kasashen Habasha, da Gabon, da Angola, da Benin, da Masar, da cibiyar kungiyar Tarayyar Afirka wato AU, da kuma cibiyar kungiyar kawancen Larabawa tun daga ranar 9 zuwa 16 ga wannan wata bisa gayyatar da aka yi masa.
A kwanakin baya, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka Liu Yuxi ya bayyana wa ‘yan jaridar CMG cewa, nahiyar Afirka tana daya daga cikin yankunan da jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta fara aiwatar da manufofin diplomasiyya, kuma Sin ta tsaya tsayin daka kan raya hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka.
Liu Yuxi ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, an raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka cikin inganci. Ana iya takaita yanayin dangantakar dake tsakaninsu wato nuna sahihanci da sada zumunta da juna, da cika alkawarin da aka yi, da kuma kiyaye bude kofa ga kasashen duniya.
Ban da wannan kuma, Liu Yuxi ya bayyana cewa, Sin ta zuba jari da hada gwiwa a kasashen Afirka don kawo moriya ga jama’arsu, idan ake son daidaita matsalar basusukan da aka baiwa kasashen Afirka, sai dai ya kamata a inganta karfin kasashen Afirka na raya kansu a dogon lokaci. Yayin da ake gaggauta raya Afirka bisa tsarin bai daya ciki har da kafa yankin yin ciniki cikin ‘yanci na Afirka da sauransu, za a inganta nahiyar Afirka a fannonin kula da kwadago, da kasuwanci, da albarkatu da sauransu, ta hakan za a inganta tattalin arzikinsu baki daya. (Zainab)