Yau Talata, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya gabatar da jawabi game da barazanar da Amurka take yi ta kara kakkaba wa Sin harajin kwastam na kashi 50%.
Kakakin ya ce, Sin na matukar adawa da hakan, kuma muddin Amurka ta aiwatar da wannan mataki, Sin za ta dauki matakin ramuwar gayya ba tare da wata-wata ba don kare muradunta.
- Hafsan Soji Ya Gana Da Shugabanni A Filato Kan Hare-haren Da Suka Yi Ajalin Mutane
- Kasar Sin Na Shirin Gaggauta Karfafa Karfinta A Bangaren Aikin Gona
Matakin harajin kwastam maras tushe da Amurka ke dauka na yi- min-na-rama, babakere ne. Kuma Sin ta riga ta dauki matakin mai da martani don kare muradunta, da kiyaye tsarin cinikin kasa da kasa da ya dace da halin da ake ciki.
Jami’in ya ce, barazanar da Amurka ke yi game da kara tsananta matakin da za ta dauka, kuskure ne dake nuna muguwar aniyarta ta dakile moriyar sauran kasashe, kuma tabbas Sin ba za ta amince ba ko kadan.
Kasar Sin ta sake nanata ra’ayinta cewa, ba wanda zai ci gajiyar tayar da zaune tsaye a goggayar ciniki, da aiwatar da manufar kariyar ciniki, don haka tana kalubalantar Amurka da ta gyara kuskurenta, tare da soke harajin da ta kakkaba mata, da daina matsa mata lamba kan tattalin arziki da ciniki, da warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari bisa turbar mutunta juna. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp