Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wang Zhigang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam (AI) yadda ya kamata, don ci gaban zamantakewar al’umma da tattalin arziki.
Wang ya shaidawa manema labarai a gefen taruka biyu dake gudana yanzu haka cewa, tasirin fasahar AI ba wai kawai ta shafi fannin fasaha ba ne, har ma da wasu bangarori. Yana mai cewa, ma’aikatar kimiyya da fasaha ta yi shirye-shirye don inganta sauye-sauye da yadda ake amfani da ita.
A nasa bayanin, ministan masana’antu da fasahar sadarwa na kasar Sin, Jin Zhuanglong, ya bayyana cewa, kasarsa za ta gina sama da tashoshin sadarwar 5G miliyan 2.9 nan da karshen shekarar 2023. Bugu da kari, za a hanzarta gudanar da bincike da bunkasa fasahar sadarwa ta 6G, ta yadda za a ci moriyar babbar kasuwar kasar Sin da cikakken tsarin masana’antun kasar. (Ibrahim Yaya)