Sinawa ‘yan sama jannati na kumbon Shenzou-15 da suka hada da Fei Junlong da Deng Qingming da Zhang Lu, sun aiko da gaisuwar bikin bazara ko sabuwar shekarar Sinawa daga tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, cikin wani bidiyo da hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta fitar jiya, wato jajibirin sabuwar shekara.
‘Yan sama jannatin 3 sun fito cikin bidiyon ne kowannensu dauke da takarda mai dauke da rubutun da suka yi. A biyu daga cikin takardun an rubuta kalmar Sinanci ta “Fu’ wadda ke nufin “fatan nasara” yayin da daya ke dauke da kalmomin fatan alheri daga tashar sararin samaniya ta Tiangong.
‘Yan sama jannatin sun kawata tashar binciken sararin samaniyar, wadda ke da nisan kilomita 400 daga doron kasa, da kayyakin ado na gargajiya na Sinawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp