• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sirrin Ci Gaban Kasar Sin: Daga Yin Kwaskwarima Da Bude Kofa Zuwa Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa

by CGTN Hausa
2 years ago

Shekaru 45 da suka gabata, yawan kudin shigar kowa ne dan kasar Sin, dalar Amurka 190 ne kacal, wanda hakan ya sa ta kasance cikin kasashe mafi karancin ci gaba a duniya.

Jimillar yawan shigi da ficin kayayyaki, fiye da dalar Amurka biliyan 20 ne kawai, kuma amfani da jarin waje ba komai ba ne. Yayin da ake fuskantar irin wannan yanayi, shugaban Sin na lokacin Deng Xiaoping ya yanke shawarar aiwatar da manufar yin “gyare-gyare da bude kofa ga waje”. Mene ne gyare-gyare? Deng Xiaoping ya yi nuni da cewa, “gyare-gyare shi ne ‘yantar da sassan da suka dace.” Mene ne bude kofa? Deng Xiaoping ya ce, “Duniya a yau, duniya ce dake bude kofa, ba zai taba yiwuwa kowace kasa ta ci gaba da zama saniyar ware ba, idan har muna son samun bunkasuwa, tilas ne mu dage wajen bude kofa ga ketare.” A karkashin shawarar Deng Xiaoping, an rubuta shirin “yin gyare-gyare da bude kofa ga waje” cikin kundin tsarin mulkin kasar a matsayin muhimmin manufar kasar Sin.

  • Sin Tana Alfahari Da Yanayi Masu Kyau Don Jawo Jarin Waje
  • Kwamitin Tsaron MDD Ya Kada Kuri’a Kan Tsagaita Wuta A Gaza

Wannan manufa ta taimaka wajen inganta tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin, ta kuma canza makomar kasar Sin ta zamani.

Shekaru 10 da suka gabata, a shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yanke shawarar zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. A cikin shekaru 10 da suka gabata, ta hanyar zurfafa yin gyare-gyare, kusan mutane miliyan 100 sun fita daga kangin fatara. A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta gina tsarin masana’antu na zamani, da sa kaimi ga “juyin -juya hali”, da aiwatar da cikakken tsarin mulki bisa jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kuma yaki da cin hanci da rashawa, da kafa tsarin makomar Sin.

A shekarar 2022, kasar Sin ta bayyana cikakken zurfafa yin gyare-gyare a matsayin wani muhimmin abin da zai sa kasar Sin ta inganta hanyar zamanantarwa da farfado da kasa.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Kara zurfafa gyare-gyare a lokaci guda cikin sauri, shi ne babban matakin bude kofa ga kasashen waje. Xi ya yi imanin cewa, bude kofa yana kawo ci gaba, yayin da rufe kofa yana haifar da koma baya. A cikin shekaru 10 da suka gabata, Xi ya ba da shawarar yin hadin gwiwa wajen raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kuma fiye da kasashe 150 da kungiyoyin kasa da kasa 30 sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa fiye da 230.

Kasar Sin ta kafa yankuna ko tasoshin ruwa na ciniki cikin ‘yanci 23. Kasar Sin ta shirya bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na farko a duniya, da baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa, da baje kolin inganta tsarin samar da kayayyaki na duniya.

Tun bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya, ya zarce kashi 30 cikin 100 cikin shekaru masu yawa.

Kasashen da suka ci gaba da masu tasowa, sun amfana matuka daga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, wanda hakan ya kara azama kan tattalin arzikin duniya. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
NIS Reshen Ribas Ta Yi Wa Jami’ai Ado Da Sabbin Mukamai Da Kaddamar Da Sabbi

NIS Reshen Ribas Ta Yi Wa Jami’ai Ado Da Sabbin Mukamai Da Kaddamar Da Sabbi

LABARAI MASU NASABA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.