Sau tari mutane sun dauka cewa duk abin da ya shafi nau’ukan abinci sai dai a ci kawai, amma a hakikanin gaskiya masana da dama na bangaren kiwon lafiya sun fitar da nazarurruka masu inganci a kan amfanin kayan abinci wajen kiwon lafiya da abubuwa da dama da suke da amfani a jikin dan adam.
Hakan kuwa ta sa wannan shafi ya taso gadan-gadan don ya tabo bangarori da dama, wadanda suka shafi harkokin tattalin kai, gyaran jiki da dukkanin tanadin da mace ke bukata wajen inganta rayuwar aurenta.
- Masu Cutar Sikari Na Fuskantar Karin Kudin Magani Da Kashi 200
- ‘PHISHING’ Sabuwar Hanyar Kutse A Facebook, WhatsApp Da Asusun Ajiyar Banki
Wadanda ke biye da mu, sun amfana da abubuwa masu yawa kan abin da ya shafi dukkanin abubuwan da muka ambata a sama. Kan haka ne, na ga dacewar kara lulawa cikin darasin. A wannan makon za mu dora ne daga inda muka tsaya.
Masana harkar kiwon lafiya sun yi bayanai dangane da muhimmancin kula da jiki kamar yadda na yi shimfida a farkon rubutun nan, musamman ga mata domin halittar mace daban yake da namiji. Matukar mata ba sa kula da jikinsu, babu shakka za su wayi gari, hatta ‘yan kananan ayyukan gida ba za su iya ba, ballantana kula da yara, uwa uba kuma gyaran dangatakan aurenta.
Za mu dan tattauna kan wasu ababen da za a iya amfani da su domin warkarwa ko kare kai daga kamuwa da wadansu cututtukan da suka shafi cutar daji, wato CANCER.
Cututtukan da sinadarin ke warkarwa, bayan ciwon daji, sun hada da:
- Cututtukan da ke kusantar hanta da koda
- Yana warkar da cutar gyambon ciki, wato ULCER
- Yana tsafatace huhu
- Yana kare mutum daga kamuwa da ciwon zuciya da hawan jini
- Yana wanke idanu (jajaye da busassun idanu).
- Yana taimakawa wajen kare masu motsa jiki daga matsalolin jijiya
- Yana warkar da zazzabin jiki
- Yana gyaran fatar jiki ya yi kyau sosai, ko da kuwa mutum yana fama da kuraje a fuska da jiki.
- Yana kawar da gyatsa ko numfashi mai wari daga baki.
- Ya na rage ciwon mara ga mata
- Haka kuma yana rage kiba matukar ragewa inda za a yi amfani da shi daidai bisa tsari.
Idan muka kalli wadannan cututtuka, wa la Allah a yi tunanin maganin sai masu kudi za su iya sayensa. Ma iya cewa kyauta ce daga Allah, magani ne da komin talaucin mutum zai iya sayensu. Abubuwa guda hudu ne a ke amfani da su wajen hadin maganin, su ne kamar haka:
Karas
Dankalin Hausa
Tuffa (Apple)
Lemun tsami.
Abu na farko da za mu yi shi ne, mu fere dankalin, bayan nan sai mu yi amfani da wuka mai kaifi wajen rede bayan Tuffa dinmu, mu kankare bayan Karas din. Bayan an gyara wadannan, sai a yi amfani da na’uran zamani mai markada kayan miya da kayan marmari a markada su daidai kamar yadda a ke matse lemo. Idan babu na’uran zamani irin Blender ko Juicer, sai mu yanyanka su kanana, har sai ya zama tamkar madarar lemo, mu yi amfani da dukkanin dabarun matse lemo domin sha.
Bayan an markada, sai a tace shi sosai, sannan a shanye shi lokaci guda. A kula, nan fa ba sai an sanya cikin Fridge ba. An fi so a shanye shi lokaci guda domin hakan ke sanya maganin aiki cikin sauri. Yanayin shan kuma yana tsari mai inganci. An fi son a sha maganin kafin karin kumallo. Kuma a bada akalla sa’a guda tsakanin shan maganin da cin abinci. Misali, idan mutum yana karin kumallo da karfe tara na safe, sai ya yi kokarin shan maganin da misalin karfe takwas daidai. Wannan ita ce ka’idar farko. Ka’ida ta biyu kuwa, tilas a bi tsarin hadin maganin, kamar yadda muka tattauna a baya. Allah Ya ba da sa’a.