Rundunar sojin ruwa ta Nijeriya, ta bayyana cewa tana aiki tuƙuru domin ƙara yawan haƙo ɗanyen mai daga ganga miliyan 1 da dubu 800 zuwa ganga miliyan 3 a kowacce rana.
Babban Hafsan Sojin Ruwa na Nijeriya, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ne, ya bayyana haka yayin ƙaddamar da aikin dakarun da ke yaƙi da masu satar ɗanyen mai ƙarƙashin Operation Delta Sanity kashi na II a Fatakwal.
- Rahoto: Sana’ar Watsa Labarai Ta Kasar Sin Ta Shiga Zamanin Cudanyar Digital Da Basira
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Mikawa Juna Sakon Murnar Sabuwar Shekara
Ogalla ya ce wannan aikin na daga cikin umarnin shugaban kasa Bola Tinubu na tabbatar da inganta fitar da mai domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Ya bayyana cewa tun bayan ƙaddamar da wannan runduna, an samu raguwar ayyukan masu satar mai da lalata bututun mai, wanda ya haifar da ƙaruwa daga ganga miliyan 1 da dubu 400 zuwa ganga miliyan 1 da dubu 800 a kowace rana.
A nasa ɓangaren, Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa na Gabas, Rear Admiral Saheed Akinwande, ya ce aikin Delta Sanity wanda aka fara a watan Janairu ya kawo babbar nasara wajen daƙile satar ɗanyen mai.
Akinwande, ya ƙara da cewa sun kama mutum 315 da ake zargi da satar ɗanyen mai tare da lalata matatun mai guda 468 da aka samar ba bisa ka’ida ba. Wannan matakin, a cewarsa, zai taimaka wajen cimma burin haƙo ganga miliyan uku a kowace rana.