Kasar Armenia ta sanar da mutuwar kusan sojojinta 50 a sabon rikicin da ya barke tsakaninta da makwabciyarta Azerbaijan a ranar Talata, irinsa na farko tun bayan kazamin yakin da bangarorin biyu suka gwabza a shekarar 2020 gabanin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta.
Bayan shafe tsawon dare ana gwabza yaki tsakanin dakarun bangarorin biyu da ya kai ga asarar dimbin rayuka, Armenia ta mika kokon barar neman taimako daga kasashen duniya don kange Azabaijan daga ci gaba da kutsawa cikin yankunanta da ke kan iyaka.
- Burina Na Canza Rayuwar Al’umma Ta Hanyar Rubutu -Zahra Zamsarf
- An Shiga Matakin Farfado Da Sassan Da Girgizar Kasa Ta Shafa A Lardin Sichuan
Kasashen biyu mambobin tsohuwar tarayyar Soviet tun bayan tsagaita wuta a yakin na 2020 daya kashe sojoji dubu 6 da 500 wannan mafi munin yaki da suka gwabza da juna duk dai kan yankin na Nagorno-Karabakh da ke kan iyakarsu.
Tuni dai manyan kasashe suka fara tsoma baki a dadaddn rikicin, inda shugaba Vladimir Putin na Rasha ya tattaunawa da ministan harkokin wajen Armenia da nufin shiga tsakani don sasantawa yayin da a bangare guda shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiyya ke gargadin kasashe da cewa kada su hasala Azerbaijan a kokarin nuna goyon bayansu ga Armenia.
Shi ma shugaba Emmanuel Macron na Faransa, yanzu haka na tattauna batun na Armenia a majalisar tsaron kasar don lalubo hanyar tallafawa kasar.
Firaministan Armenia Nikol Pashinyan, a jawabinsa gaban majalisar kasar a ranar Talata, ya ce yanzu haka dakarun kasar 49 suka rasa rayukansu a kan iyaka yayin da ya bai wa al’umma tabbacin samun taimako da kuma goyon baya daga Faransa da Rasha wadanda suka sha alwashin shiga tsakani.
Haka zalika yayin tattaunawar Firaministan da ministan harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya ba shi tabbacin shiga tsakani, yayin da ya roki kai zuciya nesa tsakanin kasashen biyu.