Dakarun Bataliya ta daya Barikin Dukku da hadin guiwar ‘Yan banga a jihar kebbi sun yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su tare da fatattakar ‘yan bindiga da dama a dajin karamar hukumar Shanga da ke Jihar Kebbi.
Nasarar da aka samu ta biyo bayan wani aikin ceto da rundunar hadin guiwa da jami’an tsaro suka yi a dajin karamar hukumar Shanga bayan rahoton wadanda aka yi garkuwa da su.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Tare Da Gano Bindigar AK47 A Kebbi
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
A cewar daraktan tsaro, AbdulRahman Usman, maza shidan da aka ceto duk sun kasance cikin koshin lafiya da kuma walwala da jin dadi kuma mayar da su cikin iyalansu.
Ya bayyana cewa dakarun Bataliya ta 1 na Dukku Barrack da ke Birinin Kebbi da ke aikin share fage tare da hadin gwiwar ‘yan banga na yankin sun kai wani samame a tsaunin Kogon Damisa da ke kusa da Saminaka a karamar hukumar Shanga, wani gari mai iyaka tsakanin Kebbi da Jihar Neja.
A cewarsa, a yayin samamen, rundunar ta fatattaki ‘yan bindiga da dama tare da ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su.
“An ba da rahoton bacewar wadanda aka ceto, an yi garkuwa da su na dan wani lokaci, kafin samun nasarar ceto su.
An sanar da jami’an tsaro a yankin da suka hada da sojoji da ‘yan banga inda suka shiga cikin dajin Shanga, an yi nasarar ceto wadanda harin ya rutsa da su.
Daraktan, ya yaba da irin namijin kokarin da sojojin ke yi, yayin da ya kuma jaddada kudirin gwamnatin Gwamna Nasir Idris na tallafa wa hukumomin tsaro a jihar don tabbatar cewa tsaro ya inganta, Inji shi.
Ya ce baya ga ci gaba da tallafin kayan aiki da gwamna ke baiwa jami’an tsaro, ya kara da cewa ” matsayin Gwamnan jihar babban jami’in tsaro na jihar ya ba da umarnin yin ga duk jami’an tsaro da su magance duk wata barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar. Inji shi.