Dakarun Runduna ta 3 Division/Operation Enduring Peace (JTF OPEP) sun cafke wani ɗan ta’adda ɗauke da bindigar AK-47, da sinƙin harsashin bindiga guda ɗaya da ƙarin wasu harsasai 11 a ƙauyen Kaskra da ke yankin Ropp a ƙaramar hukumar Barkin Ladi, jihar Filato.
A cewar sanarwar da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya fitar a ranar Alhamis, dakarun sun yi gaggawar kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa kan shirin kai hari a ƙauyukan da ke Fann District.
- Filato Ta Tsakiya Ta Amince Da Tazarcen Mutfwang A 2027
- ’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato
Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama an tura shi ne domin kai hari a yankin Nding, inda yanzu haka yake hannun jami’ai domin bayar da bayanai da za su taimaka wajen ci gaba da ayyukan sintiri da fatattakar sauran miyagu.
Zhakom ya ce Sojoji suna ci gaba da aikin kama sauran ƴan ta’adda da suka tsere tare da kwato makaman da suke dasu, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren da ke addabar al’umma a yankin.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun za su ci gaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar da kewaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp