Dakarun rundunar Operation Safe Haven a Jihar Filato, ta kama wasu safarar makamai guda biyar tare da kwace makamai da alburusai a hannunsu.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, Manjo Stephen Nantip Zhakom, ya fitar a ranar Talata, ta ce an kama makaman ne a wani samame da aka kai a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar.
- Yaƙi Da ‘Yan Bindiga: Yadda Gwamna Dauda Ya Karɓi Baƙuncin Babban Hafsan Tsaro
- Za A Gabatar Da Shagalin Bikin Zhongqiu Na CMG Na Shekarar 2024
“An fara wannan aiki ne cikin tsakiyar daren ranar 16 ga watan Satumba, 2024 zuwa safiyar ranar 17 ga watan Satumba, 2024.
“Sojojin sun kai samame a mafakar wani mai safarar makamai da aka gano da suna Mohammed Sani a yankin Ma’adinan Naraguta a Bayameni kusa da titin Bauchi a Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, inda aka kama wanda ake zargi da wasu mutane mutane,” in ji sanarwar.
Ya ce an kuma kwace makamai da alburusai masu tarin yawa a hannun wadanda ake zargin.
“A halin yanzu ana yi wa wadanda ake zargin tambayoyi don samun bayanan sirri masu amfani da za su taimaka wajen cafke sauran wadanda suke aiki tare da kuma rushe tsarin samar da makamai,” a cewarsa.